✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum tara na fama da zazzabin Lassa a Jihar Adamawa

Akalla mutum tara ne ke fama da cutar zazzabin Lassa a Jihar Adamawa kamar yadda Ma’aikatar Lafiya ta jihar ta tabbatar. Likitoci sun tabbatar da…

Akalla mutum tara ne ke fama da cutar zazzabin Lassa a Jihar Adamawa kamar yadda Ma’aikatar Lafiya ta jihar ta tabbatar.

Likitoci sun tabbatar da cewa a cikin taran, akwai biyu wadanda ke da cutar daga Karamar Hukumar Numan ne da kuma Yola ta Arewa, sannan mutum shida bayan gwajin da aka yi musu an gano cewa ba su dauke da cutar sannan daya kuma ana jiran sakamakon gwaji.

Kamar yadda rohotanni kan binciken zazzabin Lassa ya nuna daga Ma’aikatar Lafiyar Jihar a 13 ga watan Febrairu,2020, an gano cewa mutum dayan da ke fama da cutar daga kauyen Ngabalang yake na Karamar Hukumar Numan yanzu ya rasu. Rohoton ya nuna cewa daya daga cikin masu sharar asibiti da ya hadu da gawarsa ma ya kamu da cutar amma yana jinya a Asibitin Gwamnatin Tarayya (FMC) da ke Yola kuma yana samun sauki, kamar yadda Daraktar Ma’aikatar Lafiya, Dokta Bwalki Dilli ya bayyana.

Ya yi kira ga jama’a su kula wajen tsabtace muhallinsu da rufe abinci da kuma daina shanya hatsi a waje inda babu tsabta.

A halin yanzu dai akwai masu wayar da kai kan zazzabin Lassa wadanda suka ziyarci makarantu biyar da masu shayi da kuma Ma’aikatar Kananan Hukumomi inda suka wayar wa mutum 1,274 kai game da yadda za su kare kansu daga cutar da kuma inda za su nemi dauki idan an samu mai cutar a cikinsu.

Ma’aikatar Muhallin sun wayar da kan mutum 284 a gidaje 300 da ke unguwannin Demsawo da Luggere da Karewa da Nasarawo da kuma Karamar Hukumar Yola ta Arewa game da cutar.

Duk da kokarin da ake yi na wayar da kan mutane game da cutar, Unguwar Wuro Jabbe da Gadar Coci na fama da kazanta da cunkusuwar jama’a.