Masu zabe miliyan 17 sun fara kada kuri’unsu domin zabar sabon Shugaban Kasar Ghana.
An fara zaben ne da misalin karfe 7:00 na safiyar Litinin, ana kuma sa ran kammala shi da misalin karfe biyar na yamma kamar yadda jaddawalin zaben ya tabbatar.
- Zaben Ghana: ‘Yan takara sun kulla yarjejeniyar zaman lafiya
- Zaben Ghana: Obasanjo ya gargadi Akufo-Addo da Mahama
Ana sa ran kada kuri’un ne a mazabu 38,622 da ake da su gundumomin zabe 275 da ke fadin kasar
’Yan takara 12 ne suke fafatawa domin neman kujerar shugabancin kasar, ciki har da shugaba mai ci, Nana Akufo-Addo, na jamiyyar NPP da ke neman wa’adi na biyu.
Sai dai masu hasashen na ganin cewar zaben zai fi zafi ne a tsakanin Shugaban Akufo-Addo da magabacinsa, John Dramani Mahama na jam’iyyar NDC.
Duk wanda ya lashe zaben daga cikin su biyun ana sa ran zai yi shekara hudunsa na karshe ne a gidan gwamnatin Jubilee, kamar yadda tsarin mulkin kasar ya tanadar.
Sauran abokan takara
Sauran abokan hamayyar tsofaffin shugabanin kasar sun hada da Mista Christian Kwabena Andrews na jam’iyyar GUP; Madam Brigitte Akosua Dzogbenuku ta jam’iyyar PPP; Madam Akua Donkor ta jam’iyyar GFP; da Nana Konadu Agyemang-Rawlings ta jam’iyyar NDP
Sauran sun hada da: Dokta Hassan Ayariga na jam’iyyar APC; Ivor Kobina Greenstreet na jam’iyyar CPP; Henry Herbert Lartey na jam’iyyar GCPP; da kuma Percival Kofi Akpaloo na jam’iyyar LPG.
Akwai kuma Mista Alfred Kwame Walker na jam’iyyar IC; da kuma David Asibi Ayindenaba Apasera na jam’iyyar PNC.
Daga cikin ’yan takarar 12, duk wanda ya samu fiye da kashi 50 na jimlar kuri’un da aka kada, to shi hukumar zabe za ta bayyana a matsayin zababben shugaban kasar jamhuriya Ghana ta hudu.
Kazalika, ana gudanar da zaben adadin ’yan majalisa 275 da za su wakilci al’ummomin kasar a Majalisar Tarayya na tsawon shekara hudu masu zuwa.
Wannan zaben shi ne na takwas tun daga lokacin da Ghana ta bi sahun kasashen da ke bin tsarin mulkin dimokuradiyya.
Jam’iyyu biyu kacal ke yin karba-karbar mulki
A tsawon lokacin da aka kwashe, jam’iyyu biyu kacal ke ta yin karba-karbar mulkin kasar.
Jam’iyya NPP mai mulki ita ta kawo Shugaban Nana Akufo-Addo da kuma John Agyekum Kuffuor da ya mulki kasar daga 2000 zuwa 2008.
Ita kuma babbar jam’iyyar adawa ta NDC ta tsohon Shugaba John Dramani Mahama, ita ta kawo marigayi Jerry Rawlings (1992–2000); marigayi John Atta Mills (2009-2012); da kuma John Dramani Mahama (2012–2016).
Za mu gudanar da sahihin zabe —Hukumar Zabe
Shugabar Hukumar Zabe ta Ghana, Misis Jean Mensa, ta bayyana cewar hukumar za ta gudanar da sahihin zabe.
Ta yi alkawarin hukumar za ta samar da dukkanin kayan zabe da ake bukata a wadace kuma a kan lokacin.
Ta ce sun raba injinan tantance masu zabe sabbi fil guda 74,800 domin tabbatar da sahihancin zaben da kowa zai aminta da shi.
A cewarta, jami’an zaben sun kunshi ma’aikatan wucin gadi 233,632 masu tattara kuri’un, masu taimaka musu, masu tantance masu zaben, masu ba da takardun jefa kuri’a, da kuma masu sa ido domin tabbatar da an bi dokokcin cutar coronavirus.
“A kowanne akwati, mun ajiye na’urar gwajin zafin jiki da kayan wanke hannu da sauran matakan kariyar cutar coronavirus”, inji ta.
Jami’an tsaro 62,794 ne ke tsare zaben
Babban Sufeton ’Yan sandan Ghana James Oppong-Boanuh, ya ce jamia’an tsaro 62,794 ne suke tsaron zaben.
Ya ce bincikensu ya nuna akwai mazabun 6,178 a ciki 33,367 da ake da su a fadin kasar da suke da matsala.