✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum miliyan 165 sun fada kangin talauci cikin shekaru uku —MDD

An yi hasashen wasu karin miliyan 90 za su fada kasa da layin talauci na rayuwa kan dala 3.65 duk rana guda.

Cutar sankarau, annobar Covid-19, matsalar tsadar rayuwa da yakin Ukraine sun jefa mutane kimanin miliyan 165 cikin talauci tun daga shekarar 2020 a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya da su dakatar da karbar basussukan da kasashe masu tasowa ke biya domin saukaka nauyi.

Sakamakon matsalolin da aka rika cin karo da su a cikin shekaru uku da suka gabata, hasashe na nuna cewar akwai yiwuwar kimanin mutane miliyan 75 za su fada cikin matsanancin talauci, wanda aka ayyana a matsayin suna rayuwa a kasa da dala 2.15 duk rana a tsakanin 2020 zuwa karshen 2023.

Haka kuma, an yi hasashen wasu karin miliyan 90 za su fada kasa da layin talauci na rayuwa kan dala 3.65 duk rana guda, a cewar wani bincike da Hukumar Raya Kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya (UNDP) ta buga.

Rahoton ya ce matalautan sun fi shan wahala, inda aka yi hasashen samun kudin shigar su a shekarar 2023 zai kasance kasa da matakan da aka dauka kafin barkewar annobar.

A cikin wata sanarwa da shugaban UNDP, Achim Steiner ya fitar, ya ce “Kasashen da za su iya saka hannun jari a cikin ayyukan tsaro a cikin shekaru uku da suka gabata sun haura adadi mai yawa na mutane da kan iya fadawa cikin talauci.”

Sabanin haka, ya ce, “a cikin kasashe masu yawan bashi, akwai dangantaka tsakanin manyan basussuka, rashin isassun kudade na zamantakewa, da karuwar talauci mai ban tsoro.”

Rahoton ya yi kira da a dakatar da biyan bashi a cikin kasashe masu fama da matsalar tattalin arziki, “domin karkatar da biyan basussukan da ake bi wajen samar da kudaden jama’a da kuma dakile illolin tarnaki na tattalin arziki.”

A cewar wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniyar ta fitar a Larabar makon jiya, kimanin mutane biliyan 3.3 — kusan rabin bil’Adama, suna rayuwa a cikin kasashen da ke kashe kudin ruwa kan biyan bashi fiye da na ilimi da kiwon lafiya.

Haka nan kasashe masu tasowa, duk da karancin basussuka, suna biyan riba mai yawa, wani bangare saboda karin hauhawar farashin manyan Kudaden duniya da ake samu.

A cewar rahoton na UNDP, kudaden da ake kashewa domin fitar da sabbin matalauta miliyan 165 daga kangin talauci a shekara zai zarce dala biliyan 14 wato da kusan kashi 0.009 na abin da ake fitarwa a duniya.

Idan aka hada da asarar kudin shiga tsakanin wadanda suka rigaya kafin bala’in, kudin ragewa zai kai kusan dala biliyan 107, ko kashi 0.065 na ma’auni tattalin arziki GDP na duniya, in ji marubutan rahoton.

Steiner ya ce “Akwai tsadar rayuwa na dan Adam na rashin aiki wajen sake fasalin kasashe masu tasowa kan abin da ya shafi rance (bashi).”

Don haka, “muna bukatar sabbin hanyoyin da za mu iya hangowa da shawo kan matsaloli da sanya tsarin samar da kuɗade don yin  aiki ga mafi rauni a cikin al’umma.”

A farkon makon nan ne Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, wanda ke yunkurin yin garambawul ga cibiyoyin hada-hadar kudi na kasa da kasa, ya yi Allah wadai da “tsarin kudi na duniya” da ya shude, wanda ke nuna karfin ikon mulkin mallaka na zamanin da aka kirkiro shi.