Ana sa ran kimanin mutum dubu 25 ne za su halarci filin wasa na kulob din Bayern Munich da ke Jamus a karshen makon gobe don tarbar sabon koci Pep Guardiola.
Wata sanarwar da kulob din ya fitar a kafar sadarwarsa ta ce tuni kulob din ya yanke shawarar yin amfani da babban filin wasa na kasar don yin atisayen kwana biyu ganin yadda dubunan magoya baya suka nuna sha’awar halartar filin wasan don kashe kwarkwatar ido wajen tarbar sabon kocin.
Jaridar Die Welt da ke kasar ta ruwaito cewa ganin yadda dubban magoya baya suka nuna sha’awar halartar filin wasan kulob din a ranar da kocin zai karbi ragamar aiki ta sa kulob din yanke shawarar yin amfani da babban filin wasan da ya fi nasu.
Kulob din ya ce za sayar da tikin shiga filin wasan ne a kan Fam biyar kwatankwacin Naira dubu daya da dari uku a matsayin kudin shiga kuma za a yi amfani da kudin wajen tallafawa wadanda ambaliyar ruwa ta yi wa barna kwanan nan a kasar.
A ranar Litinin mai zuwa ce ake sa ran sabon koci Guardiola zai tattauna da ’yan jaridu kuma gidan talabijin na kasar ya sha alwashin watsa shirin kai-tsaye don amfanin mutanen kasar.
A watannin bayan ne dai kulob din Bayern Munich ya bayar da sanarwar daukar Pep Guardiola, tsohon kocin FC Barcelona da ke Sifen a matsayin sabon kocinsa.
A kakar wasan da ta wuce ne kulob din ya lashe kofin zakarun kulob-kulob na Turai da kofin gasar rukuni-rukuni na kasar da kuma kofin kalubale na kasar da hakan ta sa babu kulob din da ya kama kafarsa a kakar wasa ta bana.
Mutum dubu 25 ake sa ran za su tarbi sabon kocin Bayern Munich Pep Guardiola
Ana sa ran kimanin mutum dubu 25 ne za su halarci filin wasa na kulob din Bayern Munich da ke Jamus a karshen makon gobe…