✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum biyar da ka iya maye gurbin Solskjaer a Manchester United

A makon jiya ne kungiyar Manchester United ta sallami Ole Gunnar Solskjaer a matsayin mai horar da ’yan wasanta bayan kungiyar ta kwashi kashinta a…

A makon jiya ne kungiyar Manchester United ta sallami Ole Gunnar Solskjaer a matsayin mai horar da ’yan wasanta bayan kungiyar ta kwashi kashinta a hannu a wajen kungiyar Watford da ta doke ta da ci hudu da daya.

Tun watannin da suka gaba ne magoya bayan kungiyar suke ta yin kira da a sallami kocin bayan ganin yadda kungiyar ke ta kwan-gaba-kwan-baya.

Wannan ya sa Aminiya ta rairayo wasu mutum biyar da take ganin a cikinsu ne daya zai zama sabon kocin kungiyar.

Zinedine Zidane

Zidane kusan shi ne wanda aka fi jin sunansa a matsayin wanda zai maye gurbin tsohon kocin, musamman ganin nasarorin da ya samu a kungiyar Real Madrid.

Ya lashe Gasar Zakarun Turai uku da Laliga biyu a lokaci biyu da ya yi yana horar da Real Madrid.

Sai dai wasu rahotanni da ba a tabbatar ba har yanzu suna cewa Zidane har yanzu yana nuna rashin amincewa da tsarin Manchester United, wanda hakan ke nufin da wuya da ya karbi aikin horar da kungiyar.

A yanzu Zidane yana zaman hutu ne.

Zinedine Zidane  Hoto: mirror.co.uk

Brendan Rodgers

Rodgers shi ne kocin kungiyar Leicester City a yanzu haka, inda ya jagoranci kungiyar wajen lashe Kofin Kalubale a kakar bara da na Community Shield.

Ya taba horar da kungiyar Liverpool, inda a kakar bara 2014 Liverpool din ta kusa lashe Firimiyar Ingila.

Ya lashe kofuna 7 a kungiyar Celtic da ya horar.

Brendan Rodgers Hoto: thesun.co.uk

Erik Ten Hag

Ten Hag yana da cikin matasan masu horar da ’yan wasa da zamani ke yi da su a Turai a yanzu haka.

Ana yabonsa ne musamman ganin yadda ya dawo da martabar kungiyar Ajax da yake a yanzu.

A kusan duk kaka sai Ajaxa ta rasa dan wasa babba, kamar yadda ta rasa irinsu De Jong da De Light da Van de Beek, amma hakan bai hana kungiyar cigaba da taka rawar gani.

Erik Ten Hag Hoto: skysports.com

Mauricio Pochettino

Wani koci da aka dade ana maganar zai iya rike Man United shi ne Pochettino wanda a yanzu yake rike da kungiyar PSG.

Tun a shekarar 2016 ce aka fara maganar bayan kungiyar ta sallami Louis van Gaal.

Yanzu haka yana kungiyar PSG, sai ana ganin zai iya dawowa Manchester United din kasancewar magoya bayan na sonsa sosai.

Mauricio Pochettino Hoto: teamtalk.com

Michael Carrick

Michael Carrick a yanzu shi ne yake rikon horar da ’yan wasan kungiyar ta Manchester United bayan Solskjaer ya tafi.

Shi ne mataimakin Mourinho lokacin da yake horar da kungiyar, sannan ya cigaba da rike matsayin a zamanin Solksjaer.

A yanzu wasu na tunanin ya samu kwarewar da zai iya jan ragamar horar da kungiyar.

Michael Carrick Hoto: firstsportz.com