Akalla mutum tara ne aka tabbatar da rasuwarsu, uku kuma suka samu munanan raunuka a wani mummunan hatsarin mota da ya faru a kan hanyar Kano zuwa Zariya.
Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) shiyyar Kano, Zubairu Mato shine ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa a ranar Talata.
Ya ce hatsarin ya faru ne da misalin karfe 9 na safiyar Litinin inda ya rutsa da wata babbar motar daukar kaya, motar fasinja da kuma babur mai kafa uku.
Hatasarin wanda ya faru a kauyen Imawa na Karamar Hukumar Kura ya yi sanadiyyar yin taho-mu-gama tsakanin motocin guda biyu.
Zubairu ya ce motocin sun hada da wata tirela mai lambar KMC158XW da kuma karamar mota mai lamba AE884GZW sai kuma babur din da ba shi da lamba.
Ya alakanta hatsarin da tukin ganganci inda ya ce tirelar ta doki karamar motar ne a daidai lokacin da take kokarin kauce wa babur din da yake tahowa daga daya hannun.
“Mun samu kira wajen misalin karfe 9:12 na safiyar 6 ga watan Oktoba inda nan da nan muka aike da jami’anmu na ceto zuwa wurin domin ceto mutanen”, inji kwamandan.
Ya ce mutanen da hatsarin ya rutsa da su sun hada da maza biyu, mata shida sai karamin yaro daya, yayin da wasu mutum uku kuma suka samu raunuka.
Tuni dai aka garzaya da mutanen Babban Asibitin garin Kura domin ba su taimakon gaggawa.
Daga nan sai ya yi kira ga masu amfani da hanyoyi su daure su rika bin dokoki don kauce wa faruwar hadurra.
Hanyar Kano zuwa Zariya, Kaduna zuwa Abuja ta kasance tamkar tarkon mutuwa sakamakon aikin sabunta ta da ake yi wanda a wurare da yawa yakan tilasta wa masu bin ta komawa amfani da hannu daya.