✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 80 sun mutu a turereniyar karbar kayan Sallah

Lamarin ya faru ne bayan daruruwan mutane sun je karbar tallafin kayan karamar sallah.

An shiga juyayi bayan mutuwar mutum 80 ciki har da kananan yara a yayin turereniyar rabon kayan Sallah a kasar Yemen.

Mayakan Houthi da ke iko da Sanaa, babban birnin kasar sun tabbatar da aukuwar lamarin a yankin  Bab al-Yemen da ke birnin, inda daururwan mutane sun yi cikar kwari don karbar tallafin kayan karamar sallah.

Jami’an lafiya da mayakan nan Houthi sun ce an kai wadanda suka samu raunuka a turmutsutsun zuwa asibiti.

Hotuna da aka ya da a kafofin sada zumunta bayan aukuwar lamarin sun nuna mutane a kwakkwance.

Gwamnatin Yemen sun ce an tsare wasu attajirai biyu da suka dauki nauyin rabon kayan tallafin a wata makaranta.