✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 8 sun mutu a hatsarin mota a Oyo

Sai dai Hukumar Kiyaye Hadura reshen jihar ta ce mutane uku ne suka rasu, ba takwas ba.

Wani hatsarin mota da ya auku tsakanin wata Tirela da wata mota kirar Bas, ya yi sanadin rasa rayukan mutane takwas a kan titin Ife zuwa Ibadan a jihar Oyo.

Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) reshen jihar, ta bayyana rasuwar mutane uku, wanda hadarin ya ritsa da su.

A cewar wani wanda lamarin ya faru a kan idonsa, hatsarin ya faru ne tsakanin wata motar bas mai kujera 16, da kuma tirela da ta fito daga jihar Legas.

Ya ce tirelar ta samu matsalar shanyewar birki ne, wanda hakan ne ya yi sanadiyyar ta afka wa bas din.

Ya ce nan take mutane takwas suka rasu, ciki har da direban motar bas din.

Sai dai ya ta’allaka hatsarin da aikin titin da ake yi a hanyar wanda shi ne yake tilasta wa masu ababen hawa amfani da hannu daya.

Da wakilinmu ya tuntunbi kwamandan FRSC reshen jihar, Uche Chukwurah, ya tabbatar da faruwar hatsarin, sai dai ya ce mutane uku ne suka rasu.

A cewarsa, daga cikin wanda suka rasun akwai; maza biyu da mace daya.

Kazalika, Kakakin ’Yan Sandan Jihar, Gbemiga Fadeyi, shi ma ya tabbatar da cewar mutane uku ne suka rasu a hatsarin.