✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 8 sun mutu a harin da ’yan fashi suka kai wa bankuna 4 a Benuwe

Tsautsayin ya rutsa da bankuna hudu da suka hada da UBA, Stanbic, First Bank da Zenith.

Akalla mutum takwas ne suka rasa rayukansu yayin da ’yan fashi da makami suka kai hari kan wasu bankuna a yankin Otukpo da ke Jihar Benuwe.

Wakilinmu ya ruwaito cewa tsautsayin ya rutsa da bankuna hudu da suka hada da UBA, Stanbic, First Bank da Zenith.

Cikin wadanda suka rasa rai akwai ’yan sanda 3, dan sintiri daya, wani kansila a yankin da kuma masu hulda da banki guda biyu.

Rahotanni sun bayyana cewa sai da barayin suka kai farmaki kan ofishin ‘yan sanda da ke daura da bankunan kafin samun damar aukawa cikin bankunan.

Akalla sun shafe sa’a daya suna sata kafin ficewa daga yankin suna harbin iska a motocin Hilux biyu da wata karamar mota daya.

Kakakin rundunar ’yan sanda, SP Catherine Anene ta tabbatar da aukuwar al’amarin, sai dai ta ce ba ta da cikakken bayani a kai