Mayakan ISWAP sun kashe fararen hula takwas a sabon harin da kungiyar ta kai kauyen Kautakari da ke Karamar Hukumar Chibok ta Jihar Borno.
Ranar Talata da almuru ne dai mayakan ISWAP suka fara wa kauyen suna luguden wuta kan mai uwa da wabi suna banka wa gidaje wuta.
- Sojoji sun tsere bayan harin ISWAP a Chibok
- MDD ta yi alkawarin taimaka wa Borno kawo karshen Boko Haram
Majiyarmu a ce “Mun tsinci gawarwarki takwas daga wurin da aka kai harin jiya (Talata) a kauyen (Kautikari), amma har yanzu akwai dimbin mutane da ba a san inda suke ba.”
Mayakan na ISWAP sun kai harin ne sa’o’i kadan bayan ziyarar farko da Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya kai Jihar Borno.
A lokacin ziyarar da ya kai birnin Maiduguri, Guterres ya yi alkawarin bayar da gudummawa wajen ganin ayyukan ta’addanci sun zama tarihi a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.