✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 7 sun mutu bayan cin abinci mai guba a Sakkwato

Mutanen kauyen sun wayi gari cikin alhini da kuma jimamin wannan lamari da ya faru.

Wasu mutum bakwai ’yan gida daya sun mutu bayan cin wani abinci da ake zargi yana dauke da guba a kauyen Kauran Yabo da ke Karamar Hukumar Yabo a Jihar Sakkwato.

Tun a safiyar Talatar nan ce mutanen kauyen suka wayi gari cikin alhini da kuma jimamin wannan lamari da ya faru.

Ana zargin dai wani dambu ne ya yi ajalin mutanen bakwai da suka hada da matan aure biyu da kuma kananan yara biyar.

A hirar shi da Muryar Amurka, magajin gidan da abin ya faru, Mallam Umaru Kauran Yabo, ya bayyana cewa, da dare maidakinsa ta yi wani dambu na masara da kowa ya ci duk da wadanda ba gidan su ke ba, kuma ba a sami wata matsala ba.

Bisa ga cewarsa, kafin su kwanta, mai dakin ta dauki sauran tsakin da ya rage ta baza a waje domin ya sha iska ba tare da ta rufe ba.

Ya ce kashe gari ta dauki tsakin ta kara da dambun da ya rage ta sake gyarawa ta ba yara su ka ci, wandacin wannan dambun da safe ya yi sanadin mutuwarsu.

Maigidan ya bayyana cewa, ba za su tantance aininin abinda ya yi sanadin mutuwar mutanen ba, ko daga tsakin ne ko kuma sauran dambun.

Sai dai yace, sun kai mutanen da kuma sauran abinci asibiti domin a gudanar da bincike bayan da lamarin ya faru, sai dai a daidai lokacin dauko rahoton ya ce hankali ya koma kan rashin da su ka yi ba binciken sanadin ba.

A bayan nan an samu faruwar makamancin wannan lamari, domin ko a Sakkwato an samu haka a Karamar Hukumar Isa, kuma ba da jimawa ba an samu irin haka a Jihar Zamfara.

A karshen makon da ya gabata ne wasu rahotanni ke cewa wani ango da ’yan uwansa biyar sun mutu bayan cin abincin biki da ake zargi yana dauke da guba a Jihar Enugu.

Mutanen garguruwan Obollo-Eke da Udenu da kuma Aka-Utara a Karamar Hukumar Adani, Uzo-Uwani a jihar sun girgiza bayan faruwar wannan mummunan al’amari.

Angon mai suna Obinna Dieke na cikin wadanda kaddarar ta afka musu, yayin da ita ma amaryar a yanzu haka take kwance a asibiti ita da wasu mutum biyun.