✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 6 sun shiga hannu kan cin fuskar Sarkin Kano

Lamarin ya faru yayin bikin sake kaddamar da Asibitin Hasiya Bayero da ke Jihar.

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta cafke wasu mutum shida da ake zargi da cin fuskar Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Hussaini Gumel ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai ranar Litinin a Kano.

Gumel ya ce wadanda ake zargin sun yi yunkurin tunzura jama’a ne a lokacin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sake bude Asibitin Hasiya Bayero da ke Kofar Kudu a Karamar hukumar Birni da ke jihar.

Ya ce, wadanda ake zargin sun hargitsa taron, inda suka rika furta kalamai masu tunzura Sarki Aminu Bayero wanda ya halarci taron bude Asibitin da aka gudanar ranar Lahadi

A cewar Kwamishinan, wadanda ake zargin sun dinga furta kalaman “Sabon Gwamna, sabon Sarki” inda suke nuni da cewar sai gwamna Abba Kabir Yusuf ya kwance rawanin Aminu Ado Bayero ya nada wani sabon sarkin.

Gumel ya ce, ‘yan sanda sun yi amfani da fasaha wajen zakulo wadanda ke da hannu a lamarin, inda yanzu suke gudanar da bincike domin gano wadanda suka dauki nauyinsu.

“Ba a gayyaci irin wadannan wajen taron ba. Masu kutse ne da suka zo da kansu, kuma tabbas wani ne ko gungun mutane ne suka dauki nauyinsu.

“An gano mutum shida yanzu. Mun yi amfani da fasaha don gano su. Har yanzu muna nazarin faifan bidiyon kuma muna kokarin kama duk wadanda ke da hannu a lamarin.

“Sarautar gargajiya aba ce mai mutunci, kuma duk wanda ya yi kokarin kawo cikas ga al’adun gargajiya makiyin ‘yan sanda ne,” in ji shi.

Aminu Ado Bayero shi ne Sarkin Fulanin Kano na 15 daga kabilar Sullubawa.

Ya hau karagar mulki ne a ranar 9 ga Maris, 2020, biyo bayan tsige dan uwansa, Muhammad Sanusi II da Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ya yi.