Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) a Jihar Zamfara ta tabbatar da mutuwar mutum shida a Gusau, sakamakon wani hatsarin mota.
Kwamandan hukumar a jihar, Iro Danladi, ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a Gusau a ranar Talata.
- Kisan Mauludi: Iyalan mutanen da aka kashe na neman diyyar N33bn daga Gwamnati
- Kano: An kama Daraktan ma’aikatar ruwa kan karkatar da injinan rarraba ruwa
Ya bayyana cewa ya kamata a wayar da kan mutane game da gyaran tituna da ake yi a jihar.
Wadanda abin ya shafa galibin mata ne da yara kanana da ke tsallaka titi.
Danladi ya gargadi direbobi da su yi taka-tsan-tsan tare da rage gudu don guje wa yanayin da ba a shirya masa ba.
A cewarsa, duk da cewa ma’aikatan hukumar suna kan hanyoyin don saukaka zirga-zirga, amma akwai bukatar kamfanonin gine-ginen da ke gudanar da ayyukan tituna a jihar su samar da isassun alamun hanyoyin don jan hankalin masu ababen hawa da jama’a.
Ya yi kira ga gwamnati da ta fadakar da jama’a kan yadda za a yi amfani da hanyoyi a wannan lokaci na ayyukan gyaran tituna, la’akari da sauye-sauyen tsarin zirga-zirga.
Danladi ya ce ya kamata gwamnati ta dauki nauyin wayar da kan jama’a a kafafen yada labarai game da hanyoyin da ake gyara don kauce wa rasa rayuka da dukiyoyi.