✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum 599 sun kamu da COVID-19 —NCDC

An sake samun mutum biyar da cutar ta kashe a rana guda.

Hukumar Dakile Cututtuka (NCDC) ta sanar cewa karin mutum 599 sun kamu da cutar COVID-19 a ranar Laraba, yayin da adadin masu cutar ya karu zuwa 197,046.

NCDC ta ce an samu sabbin masu cutar ne daga jihohi 14 ciki har da Birnin Tarayya, Abuja.

Hukumar ta ce an samu karin mutum 232 da suka kamu da cutar a Jihar Legas, yayin da Ribas ke da 83.

Enugu 66, Oyo 28, Kaduna 25, Abuja 24, Delta 22, Akwa Ibom 19, Kwara 18, Ekiti 13, Bayelsa guda 9, Kuros Riba 9, Ogun 6, Kano 3, sai jihar Gombe na da 2.

NCDC ta ce cutar ta kashe karin mutum biyar, an kuma sallami wasu 220 da suka warke bayan kamuwa da ita a fadin Najeriya.

NCDC ta kara da cewa an yi wa mutum sama da miliyan 2.8 gwajin COVID-19 daga cikin mutum miliyan 200 da ke rayuwa a Najeriya.

%d bloggers like this: