✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 56 na kwance a asibiti bayan bullar wata bakuwar cuta a Kano

An kai mutum 30 asibiti a rana guda, ciki har da mutum takwas ’yan gida daya

Mutum 56 na kwance a asibiti sakamakon kamuwa da wata bakuwar cuta mai sa amai da fitsarin jini a Jihar Kano.

Bakuwar cutar ta bazu akalla unguwanni shida a kauyen Gwangwan da ke Karamar Hukumar Rogo, lamarin da ya jefa mazauna cikin firgiciki.

“Mun kai mutum 30 Babban Asibitin Rogo a rana guda bayan barkewar cutar; Mutum daya ya rasu; Yawancin wadanda suka kamu kuma na kokawa kan yawan kudin da suke kashewa wurin jinya,” inji wani zamaunin Gwangwan, Muhammad Tukur.

Karo na biyu cikin ’yan kwanaki, bayan bullar wata bakuwar cutar da ta kwantar da fiye da mutum 200 a Jihar, wadda ake zargin gurbataccen ruwa ko sinadarin kara armashin kayan shaye-shaye da haddasawa.

Wani magidanci da mutum takwas daga iyalan gidansa suka harbu da cutar a kauyen Gwangwan, ya ce ya girgiza, ganin yadda mahaifiyarsa da matarsa da ’ya’yan da suka kamu ba sa ko iya mikewa saboda cutar.

Ya ce ya kashe sama da N10,000 a asibitoci a Rogo da Gwarzo, amma babu alamar samun nasara.

Shi ma wani magidanci ya tabbatar cewa ’ya’yansa biyu sun harbu da cutar kuma ya kashe sama da N20,000 a asibiti duk da matsalar rashin kudin da ake fama da ita.

Muhammad ya kara da cewa, “Unguwannin da cutar ta yadu sun hada da Unguwan Rijiyan Dadi, Gwanwan Gabas, Gwangwan Yamma, Unguwar Tsarmai, Gangare, and Unguwar Kofar Fada.”

Ma’aikatan lafiya a asibitin kauyen Gwangwan da suka bukaci a boye sunayensu sun ce cutar ta fi karfin kulawar karamin asibitin, shi ya sa aka tura marasa lafiyar zuwa Babban Asibitin Rogo.

Sai dai wasu jami’ai a Babban Asibitin na Rogo da suka bukaci a sakaya sunayensu sun ce ba su da masaniyar barkewar cutar.

Amma Jami’in Kula da Bullar Annoba a Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano, ya shaida mana cewa suna da rahoton bullar bakuwar cutar.

Sai dai ya ce mutum hudu ne Ma’aikatar ta samu labarin sun harbu da cutar, kuma tuni aka ba su kulawa har an sallame su daga asibiti.