Akalla mutum 54 ne suka rasu, wasu daruruwa kuma suka samu ranuka sakamakon wani mummunan hatsarin jirgin kasa.
Hatsarin ya auku ne bayan wani jirgin fasinja ya tunture daga sauka daga layin dogo a wata gadar karkashin kasa da safiyar Juma’a.
- Malaman Kano da Ganduje sun sa zare kan rigakafin COVID-19
- 6 ga Mayu ne sabon wa’adin hada lambar waya da NIN
- Mai larurar tabin hankali ya tashi hankalin jama’a a Masallacin Harami
- Yau ake rantsar da sabon Shugaban Kasar Nijar, Bazoum
“Mutane sun yi ta karo da juna, wasu a kan wasu,” inji wata mata da ta tsallake rijiya da baya tana mai cewa, “Abin da ban tsoro matuka, wasu ma iyalai ne gaba daya a cikin jirgin,” mai tarago takwas.
Masana sun ce hatsarin jirgin kasan shi ne mafi muni a cikin shekaru 40 da suka gabata a kasar Taiwan, inji jirgin ke hanyarsa daga Taipei zuwa Taitung.
Masu aikin ceto sun garzaya zuwa wurin, inda suka yi nasarar kwashe daukacin mutanen da suka matale a cikin taragon jirgin kasar.