✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum 5 sun rasu, wasu 5 sun jikkata a hatsarin mota a Bauchi

Hatsarin ya rutsa da mutum 12, inda wasu suka mutu wasu kuma suka jikkata.

Akalla mutum biyar ne suka rasu yayin da wasu biyar din kuma suka jikkata a wani hatsarin mota da ya auku a kauyen Zaranda da ke kan hanyar Bauchi zuwa Jos.

Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) a jihar, Yusuf Abdullahi wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce hatsarin ya faru ne a ranar Juma’a biyu ga watan Disamba 2022 da misalin karfe 7:05 na yamma.

Ya ce lamarin ya ritsa ne da motoci biyar; kirar tirela DAF mai lamba BKR 271 XA da wata karamar motar kirar Ford Galaxy mai lamba USL 144 YA.

Abdullahi, ya bayyana cewa, mutum 12 ne hatsarin ya rutsa da su, inda mutum biyar suka mutu, wasu biyar kuma suka samu raunuka, ya kara da cewa an kai wadanda suka ji rauni zuwa babban asibitin Toro domin yi musu magani.

Har ila yau,. Kwamandan ya ce an ajiye gawar wadanda suka mutu a dakin ajiyar gawa na asibitin.

Kwamandan ya kara da cewa, abin da ya haifar da hatsarin shi ne gudun wuce kima da rashin kulawa da lafiyar ababen hawa.

Abdullahi, ya kuma yi kira ga direbobi da su guji wuce gona da iri wajen gudu da kuma yin tukin ganganci musamman a lokacin cunkoson ababen hawa don rage asarar rayuka.