✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum 5 sun mutu, 37 sun jikkata a hatsarin mota a Koriya ta Kudu

Mutum 37 suka jikkata sakamakon hatsarin.

Rahotanni daga kasar Koriya ta Kudu sun ce akalla mutum biyar sun mutu, 37 sun jikkata a wani hatsarin mota da ya haifar da gobara.

Hukumomin kasar sun ce hatsarin ya auku ne a Seoul, babban birnin kasar, inda wata motar daukar kaya da wata bas, suka yi taho-mu-gama.

Sai dai babu wani cikakken bayani kan abin da ya haifar da hatsarin na ranar Alhamis.

Majiyarmu ta ce hatsarin ya auku ne a babbar hanyar da ta bi ta bututu a Gwacheon da misalin karfe 1:50 na rana agogon kasar.

An ga hayaki ya turnuke inda iftila’in ya auku da kuma jami’an kwana-kwana suna kokarin kashe gobarar da ta kama.

%d bloggers like this: