Cibiyar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta sanar da samun karin mutum 407 daga jihohi 16 da Birnin Tarayya da suka kamu da cutar COVID-19.
NCDC ta sanar da sabbin alkaluman ne a shafinta na intanet a safiyar Litinin.
- Inda aka kwana game da shari’ar Nnamdi Kanu
- Ambaliyar Ruwa: Yadda Wasu Al’ummu Ke Kokarin Kare Kansu
Hukumar Kiwon Lafiya ta bayyana cewa zuwa ranar 1 ga Agusta, 2021, adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar ya kai 174,315.
Sai dai ta ce babu wanda ya mutu ba a dalilin cutar a ranar Lahadi, don haka adadin wadanda suka mutu 2,149 ne.
Jihohin da aka samu sabbin masu cutar sun hada da 407 Legas – 160, Akwa Ibom – 75, Ondo – 51, Abia – 33, Oyo-29, Kaduna – 18, Katsina -7 da Gombe-6.
Sauran su ne; Ogun – 6, Ekiti – 5, Delta – 4, Abuja – 4, Ebonyi – 3, Edo – 2, Nejan – 2, sai Bayelsa da Nasarawa kowannansu mutum daya.
Alkaluman sun hada da adadin wadanda ba a samu ba daga jihohin Kano, Osun, Filato, Ribas, da Sakkwato.
Hukumar NCDC ta ce mutum 11 kuma sun warke an kuma sallame su daga cibiyoyin killace masu cutar a ranar Lahadi, mutum 165,005 ne kuma zuwa yanzu suka warke a fadin Najeriya.
Mutum 7,151 ne ke dauke da cutar, yayin da aka yi wa mutum miliyan 2.4 gwaji.
Cibiyar ta bayyana cewa karuwar masu kamuwa da cutar COVID-19 a cikin kasar nan ana danganta shi da rashin bin matakan kariya daga cutar.