Hukumar Tsaron ta Sibil Difens (NSCDC), ta yi nasarar cafke wasu mutum hudu yayin da suke yunkurin sace wata jaririya a Jihar Zamfara.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SC Ikor Oche, ya fitar a Gusau ranar Litinin.
- Ambaliya ta halaka mutum 662, ta raba wasu miliyan 2.4 da muhallansu a 2022 – NEMA
- NAJERIYA A YAU: Kalubalen da muke fuskanta a harkar sufuri – ’Yan Najeriya
Oche ya ce an kama wadanda ake zargin ne a lokacin da suke yunkurin yin garkuwa da yarinyar mai shekara biyu a ranar 21 ga watan Janairu, 2023 a unguwar Angwan Shado da ke cikin birnin Gusau.
Ya ce, “Da yake gabatar da wadanda ake zargin a hedikwatar hukumar ta NSCDC Gusau, Kwamanda Muhammad Mu’azu, ya ce an kama wadanda ake zargin wadanda matasa ne da laifin yunkurin yin garkuwa da wata jaririya ‘yar shekara biyu mai suna Hawau Masa’ud, wadda ’yar uwarta, Umalkaidi Shahibilu (mai shekara 13) ke dauke da ita lokacin da lamarin ya faru.
“A wannan hali ne daya daga cikin wadanda ake zargin mai suna Muslim Sani, ya kwace jaririyar daga hannunta ta karfin tsiya zuwa wani kangon da abokansa suke.”
A cewar kwamandan, ’yar uwan jaririyar ce ta ja hankalin mutane wanda ya kai ga nasarar ceto jaririyar tare da cafke wadanda ake zargin.
“Binciken da aka gudanar ya nuna cewa mutanen hudu suna shiga kangon ne inda suke yin shaye-shayen miyagun kwayoyi,” in ji shi.
Kwamandan ya ce za a gurfanar da duk wadanda ake zargin a kotu da zarar sun kammala bincike.
Sai dai ya shawarci iyaye da su kasance masu taka-tsan-tsan kuma su rika lura da yanayin da ’ya’yansu ke ciki.