✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum 3 sun mutu a hatsarin mota a hanyar Abuja-Kaduna

Ganau ya tabbatar da cewar sun tarar da gawar mutum uku kwance cikin jini.

Matafiya uku ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu biyu suka samu raunuka a ranar Laraba, a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Wani mazaunin kauyen Kakau da ke kan titin Kaduna zuwa Abuja, Malam Nasir Idris, ya ce hatsarin ya faru ne sakamakon gudun ganganci.

A cewarsa, hatsarin ya faru ne sakamakon fashewar tayar motar bas din ta yi sannan ta fada wani rami.

“Ina cikin gonata da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, kwatsam sai na ji karar hayaniya.

“Yayin da na garzaya wurin tare da wasu mutanen kauye, kura ta fara lullube ko’ina. Da kura ta lafa, sai muka hangi gawarwaki uku na kwance,” in ji shi.

Sai dai Kwamandan Hukumar Kiyaye Haddura a Jihar Kaduna, bai amsa kiran wayar da aka masa ba domin jin ta bakinsa kan faruwar hatsarin.

%d bloggers like this: