Akalla mutum uku ne suka mutu a wani rikici da ya barke tsakanin kungiyoyin asiri a yankin Opu-Nembe da ke Karamar Hukumar Nembe a Jihar Bayelsa.
Bayanai sun ce an tafka kazamin fada cikin duhun dare a tsakanin kungiyoyin biyu da ke adawa da juna.
- Canjin kudi ya yi maganin masu siyasar kudi —Buhari
- NAJERIYA A YAU: Yadda Wadanda Aka Soke Rumfar Zabensu Za Su Kada Kuri’a
Sai dai babu masaniya kan dalilin da ya haifar da rikicin da aka rika musayar wuta tsakanin kungiyoyin biyu.
Wakilinmu ya ruwaito cewa a yayin rikicin, an harbe wani mai taimaka wa Shugaban Matasan Opu Nembe da budurwarsa, tare da wani mutum guda daya.
Wata majiya a yankin ta ce an yi fadan ne tsakanin matasa wadanda suka jima suna gaba da juna.
Majiyar ta ce: “Yana tare da budurwarsa kuma an kashe su duka, an kuma harbe wani mutum guda.
“Haka kuma an kai hari tare da lalata gidan shugaban matasan Opu-Nembe, Ayerite Moses.”
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Asinim Butswat, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Sai dai ya ce ba a san adadin wadanda suka mutu ba a halin yanzu.
SP Butswat ya ce tuni rundunar ta tura karin jami’an tsaro yankin domin kwantar da tarzoma.
Ya ce: “An yi artabu tsakanin kungiyoyin da ke hamayya da juna a Nembe Bassambiri a ranar 15 ga Fabrairu 2023 da misalin karfe 22:00.
“Amma ba a tantance adadin wadanda suka mutu a halin yanzu ba, sai dai ana ci gaba da bincike.”