Mutum 21 daga cikin mutum 22 da hatsarin mota ya ritsa da su a garin Misau, Jihar Bauchi, sun riga mu gidan gaskiya.
Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) rehen Jihar ta ce mutum daya ne kacal ya tsallake rijiya da baya a hatsarin bayan dayan da suka tsira tare ya cika a asibiti.
- Nuna tsiraici: Bidiyon sabuwar wakar Hausa ya ta da kura a intanet
- ’Yan bindiga sun yi garkuwa ’yan Kasuwar Kantin Kwari 18 a hanyar Aba
- An kama masu casun tsiraici a Bauchi
- Kannywood ta zama kasuwar bukata – Zango
Kwamandan FRSC na Jihar, Yusuf Abdullahi, ya ce, “Yanzu mutum 21 ke nan suka rasu a hatsarin motar. 20 sun rasu ne nan take, daya dag cikin mutum biyu da suka tsira kuma ya rasu ranar Litinin a yayin da ake jinyar shi.
“Wasu daga cikin mamatan sun samu raunuka daban-gaban, inda suka mutu nan take, wasunsu kuma sun kone kurmus,” inji shi.
Kwamandan na FRSC ya ce mutanen sun rasu ne bayan wata Hummer Bus ta kamfanin Borno Express dauke da mutum 14 ta yi taho-mu-gama da wata Golf 3 dauke da mutum takwas ciki har da kanana yara mata biyu.
Ya ce Hummer Bus din mai lamba BO89A28 ta taso ne daga Jos zuwa Maiduguri lokacin da suka yi karo da Golf 3 din mai lamba MSA759XA da ta taso daga Misau zuwa Bauchi.
Kwamandan na FRSC ya ce an kai dukkannin gawarwakin Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU-TH), da ke Bauchi, inda a nan ake jinyar wanda ya samu raunin.
Ya yi wa Kamfanin Dillancin Labaru na Najeriya (NAN) bayani cewa a ranar Litinin ce mutum dayan ya rasu sakamakon raunin da ya samu daga hatsarin na ranar Lahadi.
Abdullahi, ya ce hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin masu amfani da tituna na kiyaye dokokin hanya domin kare rayuka da dukiyoyi.