Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC), ta ce akalla mutum 20 sun mutu sakamakon hadurran da suka auku a hanyar Ibadan zuwa Legas hadi da garin Mokwa a Jihar Neja.
Hukumar ta ce mutum 10 sun mutu, shida sun jikkata daga cikin 18 da hatsari ya rutsa da su a Ibadan, yayin da 10 sun rasu a hatsarin da ya uku a garin Makwa, Jihar Neja.
- Na daina jin dadin rayuwa, burina in cika da imani kawai – Aminu Dantata
- ’Yan bindiga sun harbe sojar ruwa, sun sace danta a Jos
Mukaddashin Shugaban hukumar na kasa, Mista Dauda Biu, shi ne ya bayyana hakan cikin sanarwar da ya fitar ta bakin jami’in wayar da kan jama’a na hukumar, Mista Bisi Kazeem ranar Talata a Abuja.
Biu ya nuna damuwarsa kan yadda masu abubuwan hawa ba su kiyaye dokokin amfani da hanya da kuma gudun wuce hankali.
Ya gargadi masu wannan hali su daina ko kuma su fuskanci fushin hukumar.
Ya ce, galibin hadurran da suka aukun, hakan ta faru ne saboda rashin kiyaye dokokin hanya.