Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) ta ce kimanin mutane 4,794 ne suka rasa rayukansu sakamakon hatsarin mota a Najeriya a shekarar 2020.
Hukumar ta ce a cikin shekarar, an sami hadurra kimanin 10,552 wanda ya rutsa da ababen hawa 17,614.
- Mutum 23 sun rasu, 33 sun ji rauni a hatsarin tirela a Neja
- Sarkin Daura ya rasa dan uwansa a hatsarin mota
Jami’in wayar da kan jama’a na hukumar, ACM Bisi Kazeem ne ya bayyana hakan a cikin wata tattaunawarsa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya, (NAN) a Abuja ranar Alhamis.
A cewarsa, akalla mutane 28,449 ne suka sami manyan raunuka, yayin da sama da 29,808 kuma suka sami kananan raunuka.
Sai dai ya ce an sami karuwar hadurran a 2020 in an kwatanta da shekarar da ta gabaceta ta 2019.
Ya ce, “Jimillar adadin hadurran da aka samu a 2020 ya karu zuwa hadurra 565, wanda yake nuna karin kaso 5.37 cikin 100.”
Bisi ya ce hukumar ta lura yawancin abubuwan da suke haddasa hadurran na da alaka ne da gudun wuce sa’a, wanda ya kawo kusan kaso 62 cikin 100 na hadurran.
Sauran dalilan dake haddasa hadurran a inji shi sun hada da tukin ganganci, shan giya kafin fara tuki, gudun da ya wuce kima, shanyewar birki, fashewar taya, bin hannun da ba na matuki ba da kuma karya dokokin hanya.
Bisi ya kuma ce duk da haka idan masu amfani da hanya suka kiyaye dokokinta akwai yuwuwar a magance samun hadurra a kasa.