✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 20 sun kone kurmus a hatsarin mota a Oyo

Mahukunta a Jihar Oyo sun tabbatar da mutuwar mutum 20, da ceto wasu biyu a hatsarin mota.

Akalla mutane 20 ne suka kone kurmus bayan wasu motocin haya biyu sun yi taho-mu-gama a ranar Juma’a.

An yi hatsarin ne a daidai mahadar garuruwan Lanlate da Maye da ke Jihar Oyo, a tsakanin wata mota kirar Sienna da wata bas da dukkansu dauke da fasinjoji.

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, Shugaban Karamar Hukumar Ibarapa ta Gabas, Honorabul Gbenga Obalowo wanda ya jagoranci jami’an gwamnati zuwa wajen hatsarin, ya ce, “Mun kirga gawarwakin mutane akalla 20 da suka kone kurmus a wannan hadari.”

Ya ce motocin biyu da kowanne ya ke tafiya a kan hanyarsa sun yi karo da juna ne inda a nan take suka kama da wuta.

Mutane biyu ne kadai aka ceto da raunuka a sassan jikinsu, aka garzaya da su zuwa Asibitin Awojobi da ke garin Eruwa domin ceton rayukansu.

Honorabul Gbenga Obalowo ya nuna alhini da tausayin ganin yadda fasinjojin suka kone kurmus ta yasda ba za a iya gane su ba.