Akalla mutane 20 ne suka kone kurmus bayan wasu motocin haya biyu sun yi taho-mu-gama a ranar Juma’a.
An yi hatsarin ne a daidai mahadar garuruwan Lanlate da Maye da ke Jihar Oyo, a tsakanin wata mota kirar Sienna da wata bas da dukkansu dauke da fasinjoji.
- Yadda aka yi kuskuren harbin wani mutum a Zariya
- Gani Ya Kori Ji: Hotunan muhimman abubuwan da suka faru a wannan mako
Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, Shugaban Karamar Hukumar Ibarapa ta Gabas, Honorabul Gbenga Obalowo wanda ya jagoranci jami’an gwamnati zuwa wajen hatsarin, ya ce, “Mun kirga gawarwakin mutane akalla 20 da suka kone kurmus a wannan hadari.”
Ya ce motocin biyu da kowanne ya ke tafiya a kan hanyarsa sun yi karo da juna ne inda a nan take suka kama da wuta.
Mutane biyu ne kadai aka ceto da raunuka a sassan jikinsu, aka garzaya da su zuwa Asibitin Awojobi da ke garin Eruwa domin ceton rayukansu.
Honorabul Gbenga Obalowo ya nuna alhini da tausayin ganin yadda fasinjojin suka kone kurmus ta yasda ba za a iya gane su ba.