Akalla mutum biyu sun rasu, kusan 80 kuma sun jikkata yayin turereniya a filin kwallon kafar birnin Basra da ke Kudancin Iraqi, gabanin wasan karshe na gasar cin kofin kasashen yankin Gulf.
Ministan Harkokin cikin Gidan na Iraqi ya shaida wa gidan talabijin na Aljazeera cewa akalla mutum biyu sun rasu, kusan 80 sun jikkata a yayin turereniyar ta ranar Alhamis.
- Kaduna 2023: Zan sauya wasu manufofin El-Rufa’i idan na ci zabe– Uba Sani
- Fira Ministar New Zealand, Jacinda Ardern, za ta sauka daga mukaminta
Kasar Iraqi mai masaukin baki dai an shirya za ta fafata da kasar Oman a wasan karshe na gasar da misalin karfe 7:00 na daren Alhamis.
Dubban ’yan kallon da ba su sayi tikitin kallon wasan ba ne suka yi cincirindo a wajen filin wasan tun da Asuba domin kallon wasan.
Wani mai daukar hoto na Kamfanin Dillancin Labaran Faransa (AFP) ya ce har zuwa lokacin da turereniyar ta faru, kofofin filin a rufe suke, yayin da motocin daukar marasa lafiya suka isa wurin da nufin ƙasar marasa lafiya zuwa asibiti.
An dai fara gasar ce a ranar shida ga watan Janairun da kungiyoyi daga kasashen yankin Gulf shida na Bahrain da Kuwait da Oman da Qatar da Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa da Yemen da kuma Iraqi.
Wannan ne dai karo na farko da kasar Iraqi take karbar bakuncin gasar tun 1979.