Wata motar dakon mai ta yi bindiga a safiyar Laraba a kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan in da mutum 2 su ka rasa ransu.
Motar dakon man ta yi bindiga ne da misalin karfe 6:05 bayan da take makare da mai a ciki a daidai kofar kamfanin sarrafa ’tiles’ na CDK da ke bayan ofishin Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) a kusa da mahadar Titin Shagamu.
- Mahara sun kona ofishin yakin neman zaben Atiku a Gombe
- Ranar Hijabi: Fitattun mata da aka yi wa tambari a duniya
Hadarin ya rutsa da motoci uku da babur guda daya inda mutane takwas suka samu munanan rauni biyu kuma suka rasa rayuwarsu gaba daya.
Mai magana da yawun Hukumar Kiyaye Hadurra na Jihar Ogun, Florence Okpe, ya tabbatar da faruwar al’amarin a garin Abeokuta, inda ya ce ana kyautata zaton gudun da motar take yi ne ya haddasa mummunan hadarin.
“Jami’an kashe gobara sun samu nasarar kashe wutar, sannan jami’anmu sun tsaya a wajen da lamarin ya faru domin ci gaba da gyaran hanya har zuwa lokacin da za a kawar da komai daga kan hanya” a cewar Okpe.
Daga karshe ya yi kira da masu ababen hawa da su kasance suna bin dokokin tuki a koyaushe tare da bin dokokin da kaidojin hanya.