Hatsarin mota ya yi ajalin mutum biyu, wasu hudu sun jikkata a Babbar Hanyar Legas zuwa Abekuta a ranar Asabar.
Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) na Jihar Ogun, Ahmed Umar ya ce hatsarin ya auku ne bayan wata mota kirar Nissan ta yi taho mu gama da wata babbar mota kirar Mack da misalin karfe 6 na safe.
- Ina tausaya wa ’yan Najeriya kan halin da suke ciki —Buhari
- Sojoji sun juyin mulki karo na biyu cikin watanni takwas a Burkina Faso
Ya ce Nissan din mai lamba KTU142XH ta yi karo da Mack din mai lamba T-12736LA da aka ajiye ne a daidai Iyana Egbado da ke Itori a kan babbar hanyar.
Bayyana cewa babbar motar ta yi faci ne kafin daya motar ta zo ta yi karo da ita.
Ya ce mutum daya ya fita ba tare da mokai ya same shi a hatsarin ba, wadanda suka jikkata da mamatan kuma an kai su wani babban asibiti domin samun kulawa.
Ya jajanta wa iyalan wadanda hatsarin ya ritsa da su, tare da cewa su tuntubi hukumar domin samun karin bayani kan abin da ya faru.
Ya kuma shawarci mutane da su guji ajiye motoci barkatai a gefen hanzya, “Idan mota ta samu matsala ko ta lalace ya kamata a sanya alama da ta dace domin masu zuwa su sani.”