Gwamnatin Jihar Binuwai ta tabbatar da rasuwar mutum biyu wasu mutum 17 kuma sun harbu da cutar zazzabin Lassa.
Kwamishinan Lafiya na jihar, Dokta Joseph Ngbea ne ya shaida wa taron manema labarai haka makon wayar da kan cutar zazzabin Lassa a Makurdi, babban birnin jihar.
- Tsoffin kudi: Gwamnati ta bukaci Kotun Koli ta yi watsi da hukuncin da ta yanke
- NAJERIYA A YAU: Yadda ’Yan Takara Ke Kashe Kudi A Lokacin Zabe
Ya bukaci mazauna jihar da su dauki matakan kawar da beraye daga muhallinsu sannan ya shawarci ma’aikatan lafiya da su rika bin matakan kariya daga cutar da sauran cututtuka masu yaduwa a tsakanin jami’an lafiya.
Ngbea ya bayyana cewa zazzabin Lassa ya fi cuta mai karya garkuwar jiki (HIV) kisa da kashi 11.7 cikin dari.
Kwamishinan lafiyar, ya ce hanya daya tilo ta dakile yaduwarta, ita ce ta tsaftar muhalli.
Ya ce gwamnatin jihar ta sayo magungunan da suka don kula da wadanda suka harbu da ita.
Ya kuma yi kira ga wadanda ke jin wani yanayi ko alamomin cutar da su ziyarci asibiti don a gwada su.