✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum 19 sun mutu bayan motar fasinja ta fada rafi a Pakistan

Lamarin ya faru ne sakamakon ruwan saman da aka tafka

Wata mota ta fado daga saman wani tsauni inda ta fada wani rafi a Kudu maso Yammacin Pakista, inda ta kashe 19 daga cikin fasinjojinta, wasu 12 kuma suka jikkata.

Hukumomin kasar dai sun ce lamarin ya faru ne ranar Lahadi, sakamakon wani mamakon ruwan sama da aka tafka.

Mahtab Shah, Mataimakiyar Magajin Garin Shirani da ke lardin Balochistan na kasar, ta ce akalla fasinjoji 35 ne a kan motar, kuma suna kan hanyarsu ce daga babban birnin kasar na Islamabad zuwa birnin Quetta.

Sai dai ana fargabar akwai yiwuwar adadin mutanen da za su mutu ya karu sakamakon yawancin wadanda suka jikkata na cikin mawuyacin hali.

Ta kuma ce tuni ma’aikatan ceto suka dukufa aikin neman ragowar masu rai daga cikin motar wacce ta yi kaca-kaca.

Mahtah Shah ta kuma ce motar ta zame ne daga kan hanya sakamakon ruwan saman da aka tafka, inda motar ta kwace masa sannan ta fada cikin rafin mai zurfin kusan kafa 200.

Ko a watan da ya gabata dai sai da akalla mutum 22 suka mutu bayan wata karamar mota ita ma ta fada cikin wani rafin a yankin na Balochistan.