✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum 19 sun mutu a hatsarin mota a Yobe

Duka fasinjoji da direbobin motocin sun rasu a hatsarin na taho-mu-gama.

Mutum 19 sun rasu a wani hatsarin mota da ya afku ranar Alhamis a Karamar Hukumar Fune ta Jihar Yobe.

Kakakin ’yan sandan jihar, ASP Dungus Abdulkarim, ya tabbatar wa Kamfanin Dillacin Labaran Najeriya  (NAN), a Damaturu cewa daukacin fasinjoji da direbobin motocin sun mutu a hatsarin.

Ya ce hatsarin ya faru da ne misalin karfe 11 na safe tsakanin wasu motoci biyu: “Daya daga cikin direbobin ya baro hannunsa saboda guje wa cunkoso wanda hakan kuma ya haddasa hatsarin.

“Bai jima da barin hannunsa ba ya yi taho mu gama da wata mota mai lamba BKD 47 SB, wadda take a kan hannunta.

“Duka fasinjojin motar da direbobin sun mutu nan take,” cewar Abdulkarim.

Ya ce an ajiye gawarwakin matafiyan a Babban Asibitin Damaturu, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da bincike.

Ya shawarci masu ababen hawa da su kasance masu bin dokokin tuki da hanya tare da daina yin gudun wuce kima, wanda hakan ke haddasa salwantar rayuka a lokuta da dama.

%d bloggers like this: