Ma’aikatan Hukumar Kwana-Kwana a Kasar Senegal sun tabbatar da mutuwar mutum 19 yayin da wata mota kirar bas da wata babbar mota suka yi karo da juna a Arewacin kasar.
Mutum 25 ne suka jikkata a hatsarin a ranar litinin, wanda ya afku a kusa da Sakal a yankin Louga, kamar yadda wata majiya ta shaida wa Kamfanin Dillacin Labarai na AFP.
- Za mu kare martabar dimokuradiyya a Zaben 2023 —DHQ
- Hana acaba a Legas ya kawo wa ‘sana’armu’ cikas – Dan fashi
A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na twitter, Shugaba Macky Sall ya ce, “Wani mummunan hatsari da ya auku mutum 19 ne suka rasa rayukansu.”
Hatsarin mota ya zama ruwan dare a kasar Senegal, musamman saboda yadda direbobi ke gudun ganganci da kuma rashin kyawun tituna.
Kasar Senegal ta shiga zaman makokin kwanaki uku bayan da wasu motocin bas guda biyu suka yi karo da juna a ranar 8 ga watan Janairu a yankin Kaffrine da ke tsakiyar kasar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutum 40 tare da jikkata wasu fiye da 100.