Akalla mutum 19 ne suka mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya faru a Bagauda da ke Karamar Hukumar Bebeji ta Jihar Kano, kamar yadda Hukumar Kiyayaye Hadura ta Kasa (FRSC) ta tabbatar.
Kazalika, hukumar ta kuma tabbatar da cewa wasu fasinjoji 19 sun ji munanan raunuka a sakamakon hatsarin.
- Ba na hanzarin yin takarar shugaban kasa a 2023 —Kwankwaso
- Mahara sun kashe fasinja 2, sun sace 40 a Taraba
A cewar Kwamandan shiyya na hukumar a Jihar Kano, Mato Zubairu, hatsarin ya faru ne da misalin karfe 7:25 na safiyar Alhamis, lokacin da motocin biyu, wadanda ke dauke da fasinjoji 45 suka yi taho-mu-gama a kusa da Makaratantar Horar da Lauyoyi ta Najeriya (NLS) da ke Bagauda.
Ya ce, “Ofishinmu na shiyya da ke Chiromawa ya samu kiran gaggawa wajen misalin karfe 07:30 na safiyar Alhamis cewa wasu motoci guda biyu kirar Hayis da ke dauke da fasinjoji 45 sun yi hatsari a Bagauda, daidai makarantar NLS.
“A cikin minti biyar, jami’an hukumarmu suka isa wajen sannan suka fara aikin ceto mutane.
“Motocin guda biyu masu lambobin KBT 152 XA da kuma NSR 275 ZX ne hatsarin ya ritsa da su. A sakamakon haka, 19 daga cikinsu sun mutu nan take, yayin da ragowar mutum 26 kuma suka ji raunuka,” inji shi.
Kwamandan ya kuma ce tuni aka garzaya da mutanen zuwa Babban Asibitin garin Kura da ke Jihar, yayin da gawarwakin wadanda suka mutu kuma aka sada su da iyalansu ta hannun ’yan sanda domin a yi musu jana’iza.
Kazalika, ya ce motocin da hatsarin ya shafa kuma an damka su ga ofishin ’yan sanda da ke Bebeji a Jihar.