✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 18 sun kone kurmus a hatsarin mota a Bauchi

Fasinjojin motar sun kone kurmus babu wanda ya tsira.

Akalla mutum 18 ne suka kone kurmus a wani hasarin mota da ya rutsa da wata mota kirar Hiace bas da tirela a kauyen Nabardo a kan hanyar Bauchi zuwa Jos.
Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) a Jihar Bauchi, Yusuf Abdullahi, ya shaida wa Aminiya cewar hatsarin ya faru ne da misalin karfe 4:40 na yamma a ranar Laraba.
“Abun takaici shi ne direban da duk fasinjojin motar sun kone kurmus.
“Hatsarin ya faru a cikin daji wajen da babu kowa ballantana a kawo wa wadanda abun ya rutsa da su dauki.
“Hatsarin yana aukuwa wuta ta tashi nan take, motar da duk wadanda ke cikinta suka kone kuma babu wanda za a iya ganewa,” in ji shi.
Abdullahi ya ce rundunar ‘yan sandan Najeriya za ta yi musu jana’iza ta bai daya.