Akalla mutum 18 ne suka kone kurmus a wani hasarin mota da ya rutsa da wata mota kirar Hiace bas da tirela a kauyen Nabardo a kan hanyar Bauchi zuwa Jos.
Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) a Jihar Bauchi, Yusuf Abdullahi, ya shaida wa Aminiya cewar hatsarin ya faru ne da misalin karfe 4:40 na yamma a ranar Laraba.
- Zan kayar da Zulum cikin sauki —’Yar takarar gwamna
- China na yi wa Duniya nuku-nuku kan alkaluman Coronavirus —WHO
“Abun takaici shi ne direban da duk fasinjojin motar sun kone kurmus.
“Hatsarin ya faru a cikin daji wajen da babu kowa ballantana a kawo wa wadanda abun ya rutsa da su dauki.
“Hatsarin yana aukuwa wuta ta tashi nan take, motar da duk wadanda ke cikinta suka kone kuma babu wanda za a iya ganewa,” in ji shi.
Abdullahi ya ce rundunar ‘yan sandan Najeriya za ta yi musu jana’iza ta bai daya.