✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum 174 sun rasu, 180 sun jikkata a turmutsutsu a Indoensiya

Mutum 174 sun rasu wasu 180 sun samu raunuka sakamakon wani turmutsutsu a lokacin da ake buga wasan kwallon kafa a kasar Indoensiya.

Mutum 174 sun rasu wasu 180 sun samu raunuka sakamakon wani turmutsutsu a lokacin da ake buga wasan kwallon kafa a kasar Indoensiya.

As samu turmutsutsu ne bayan kungiyar Arema FC ta yi rashin nasara a hannun Persebaya Surabaya a wasansu na ranar Asabar da dare a filin wasan Kanjuruhan da ke Malang a Gabashin yankin Java.

Mummunan lamarin ya auku ne bayan da ’yan sanda sun harba hayaki mai sa hawaye ga dubban fusatattun ’yan kallon da suka kutsa cikin filin wasan.

Rikicewar mutane bayan bayan harba hayaki ma isa hawayen ya sa mutanen da ke filin wasan suka ya doshi kofa domin su fice, inda a garin turmutsutsun mutane da dama suka suke, wasu da kuma aka tattake su.

Rahotannin farko sun nuna mutum 130 ne suka rasu, kafin daga bisani hukumomin kasar suka sanar da karuwar adadin zuwa 174, baa ga wasu 11 da suka ji munananan raunika.

Shugaban kasar Indonesiya,  Joko Widodo, tuni a ya bayar da umarnin dakatar da duk manyan wasanni gasar kwallon ƙafa ta kasar har sai an gudanar da bincike.