Mutum 174 sun rasu wasu 180 sun samu raunuka sakamakon wani turmutsutsu a lokacin da ake buga wasan kwallon kafa a kasar Indoensiya.
As samu turmutsutsu ne bayan kungiyar Arema FC ta yi rashin nasara a hannun Persebaya Surabaya a wasansu na ranar Asabar da dare a filin wasan Kanjuruhan da ke Malang a Gabashin yankin Java.
- NNPC ya saye gidajen mai 380 da kamfanin Oando
- Boko Haram ta kashe malaman makarantu 2,295 daga 2009 zuwa 2022
Mummunan lamarin ya auku ne bayan da ’yan sanda sun harba hayaki mai sa hawaye ga dubban fusatattun ’yan kallon da suka kutsa cikin filin wasan.
Rikicewar mutane bayan bayan harba hayaki ma isa hawayen ya sa mutanen da ke filin wasan suka ya doshi kofa domin su fice, inda a garin turmutsutsun mutane da dama suka suke, wasu da kuma aka tattake su.
Shugaban kasar Indonesiya, Joko Widodo, tuni a ya bayar da umarnin dakatar da duk manyan wasanni gasar kwallon ƙafa ta kasar har sai an gudanar da bincike.