✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 17 sun rasu wajen rububin kudi a unguwar Hausawan Kalaba

Lamarin ya faru ne a Unguwar Hausawa da ke Layin Bagobiri a birnin Kalaba

Kusan mutum 17 ne ake zargin sun gamu da ajalinsu yayin da wasu 15 suka samu munanan raunuka a Unguwar Hausawa da ke Layin Bagobiri a birnin Kalaba ranar Talata da ta gabata.

Ganau ya shaida wa Aminiya cewa, “An ware ranaku uku na bikin nuna al’adu ana hawa manyan babura da kuma sauran al’adu.

To an fito ana kallo sai wani ya bullo da mota, ya watsa kudi. To wajen rububin kwasar kudin ne akalla mutum 17 suka rasu, sannan sama da 15 suna asibiti.”

Lamarin ya faru a yammacin ranar, sannan aka kwashi wadanda suka ji rauni zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Kalaba da kuma Asibitin Sojan Ruwa.

Daga baya an sallamo wadanda suka samu sauki, sannan aka tafi da wadanda suka samu karaya zuwa Arewa domin a yi musu dorin gargajiya.

Gwamnatin Jihar Kuros Riba ta sanar da cewa ta dauki nauyin jinyar wadanda suka samu raunukan.

Haka kuma a shekaranjiya Laraba, Kwamishinan Yada Labarai na Jihar ya wakilci Gwamnan Jihar domin jajanta wa al’ummar Unguwar Hausawan da abin ya faru.

“A duk abin da ya faru, mai motar da ya haddasa hadarin ba ya daga cikin ayarin da ya kamata su je wajen,” inji shi, inda ya ce za su bincika tare da daukar mataki a kai.

Kwamandan FRSC, Maikano Hassan ya tabbatar da rasuwar mutum 1.