’Yan sanda a Afirka ta Kudu sun tabbatar da mutuwar akalla mutum 17 a wajen wani kade-kade da raye-raye da ke birnin East London na Kudancin kasar.
Shugaban ’yan sanda na lardin, Cif Birgediya Thembinkosi Kinana, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa (AFP) cewa, “Mun sami rahoton akalla mutum 17 sun rasu a wani wajen sharholiya da ke wajen shakatawa a birnin East London na Afirka ta Kudu.
- Labaran ma’aurata: Na rufa masa asiri sai na tarar da farin ciki
- Gwamnatin Zamfara ta umarci mutane su mallaki bindigogi
“Har yanzu muna kan gudanar da bincike don gano musabbabin hatsarin,” inji shi.
Ya ce galibin wadanda suka mutun ’yan tsakanin shekara 18 zuwa 20 ne.
Wasu hotunan da aka yada a kafafen sada zumunta na zamani sun nuna gawarkwakin mutanen shimfide a kasa ba tare da wata alamar rauni a jikinsu ba.
Kazalika, wasu tashoshin talabijin din kasar sun nuna jami’an ’yan sanda suna kokarin kwantar da hankulan mutanen da suka yi cincirindo a wajen gurin kade-kaden.
Birnin na East London dai wanda ke gefen tekun Indiya, na da nisan kusan kilomita 1,000 daga birnin Johannesburg na kasar. (AFP)