✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 17 sun yi rauni lokacin da jirgin kasa ya fada kogi

Jirgin ya saba hanya inda ya zarce tare da tsundumawa cikin wani kogi.

Wani jirgin kasa mai dauke da kananan yara da matasa, wadanda adadinsu ya kai akalla 50, ya kauce hanya ya fada cikin wani kogi a kasar Austria.

Kwamandan masu ba da agajin gaggawa na birnin Salzburg, Anton Schilcher, ya ce mutum 17 ne suka yi rauni a hatsarin a ranar Juma’a.

  1. Za a nemi Kannywood a rasa in dai… —Naburaska
  2. An gano wani sabon nau’in COVID-19 a Najeriya

Hatsarin ya faru ne ‘yan mintuna kadan bayan karfe 7:00 na safiyar Juma’a (karfe 6.00 ke nan agogon Najeriya) kusa da Kendlbruck.

An rawaito cewa jirgin kasar ya nutse kimanin mita hudu a cikin kogin.

A cewar kwamnadan masu aikin ceton, an rufe layukan dogo bayan faruwar lamarin har zuwa nan da wani lokaci.

An bayyana cewa jirgin na dauke da mutum 50 a lokacin da ya tsunduma cikin kogin.

Kungiyar ba da agaji ta Red Cross ma ta kai dauki wajen, inda ta bayyana cewa jirgin na kan hanyarsa ta zuwa yankin Tamsweg.

Tamsweg wani wuri ne na musamman da yara da ‘yan makaranta ke zuwa yawon bude ido a lokuta daban-daban.