✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 16 sun mutun 30 sun jikkata a hatsarin tirela a Jos

Wata tirela makare da kaya da mutane ta yi adungure, inda mutum 16, wasu kimanin 30 suna samu raunuka a hanyar Jos-Abuja

Mutane 16 sun rasu, wasu 30 sun samu rauna a hatsarin babbar mota a yankin Jos da ke Jihar Fila

Wata tirela makare da kaya da mutane ce ta yi adungure ta fada a wani rami, inda mutum 11 suka rasu nan take, wasu kimanin 30 suna samu raunuka.

Kwamndan Hukumar Kiae Haddura a Kasa (FRSC) a jihar Filato, Alphonsus Halim Godwin ya ce, “karin wasu 5 sun rasu daga bisani a asibiti.”

Jami’in ya bayyana cewa motar ta fito ne daga Jihar Kano za ta Abuja, lokacin da ta samu hatsarin a Hauwan-Kibo da ke Karamar Hukumar ta Jos Kudu.

Alphonsus ya ce wasu daga cikin wadanda suka samu raunin an kai su asibitin sojoji, wadanda suka samu rauni mai tsanani kuma an kai su Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUH).

Ya ce hatsarin ya auku ne sakamakon tsinkewar burkin motar wadda ke dauke buhunan hatsi. 

Da haka ta roki matafiya da su guji neman saukin kudin mota sa ya sa a loda su a cikin motocin daukar kaya