✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum 16 sun mutu, 21 sun jikkata a hatsarin mota a Turkiyya

Mutum 16 ne sun mutu, wasu 21 sun jikkata a hatsarin wata bas da wata motar daukar marasa lafiya da motar kashe gobara a kasar…

Mutane 16 ne suka mutu, wasu 21 suka jikkata a wani hatsari da ya rutsa da wata bas da da wata motar daukar marasa lafiya a Kudu maso Gabashin Turkiyya.

Gwamnan lardin Gaziantep, Davut Gul ya ce an samu asarar rayuka da jikkata ne bayan hatsarin wata bas da motar kashe gobara da motar daukar marasa lafiya… tsakanin yankunan Gaziantep da Nizip.”

“Ma’aikatan kashe gobara uku, ma’aikatan gaggawa biyu da ’yan jarida biyu na daga cikin wadanda suka mutu,” in ji gwamnan Gaziantep.

Kafofin yada labarai na cikin gida a kasar sun ce adadin mamatan ya haura 16 da gwamnan ya bayar.

Kamfanin dillancin labarai na DHA ya ce motar daukar marasa lafiya da motar kashe gobara da kuma wata motar bas da ke dauke da ’yan jarida sun yi karo da wata motar bas din fasinja.

Hotunan DHA ya fitar sun nuna bayan motar daukar marasa lafiyar ta yage da tarkacen karafa da ke zagaye da shi.