✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 15 sun mutu bayan Jirgin sama ya fado kan wani gida a Kazakhstan

Wani jirgin sama da yi hadari ya fado kan wani gida a Kazakhstan, inda akalla mutum 15 suka mutu sannan wasu da dama suka jikkata.…

Wani jirgin sama da yi hadari ya fado kan wani gida a Kazakhstan, inda akalla mutum 15 suka mutu sannan wasu da dama suka jikkata.

Jirgin dai na Bel Air ya taso ne daga Almaty  da misalin karfe 7:05 na safe (01:05 GMT)  birnin da ya fi kowanne girma a Kazakhstan, inda ya tunkari Nur-Sultan, babban birnin kasar to amma sai ya rikito jim kadan bayan tashinsa.

Jirgin saman yana dauke da fasinjoji 100, amma wasu rahotanni sun bayyana cewa, fasinjoji 60 ne suka tsallake rijiya da baya yayin da a yanzu haka suke karbar magani a asibiti.