✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 15 sun mutu, 7 sun jikkata a hatsarin mota a Bauchi

Hatsarin motar ya rutsa da mutum 22.

Mutum 15 suka mutu a wani mummunan hatsarin mota a kauyen Nabordo da ke Karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi.

Mista Yusuf Abdullahi, Babban Kwamandan Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) ne, ya sanar a Bauchi cewa cewa wasu mutum bakwai sun samu munanan raunukaa hatsarin da ya rutsa da wasu motoci biyu.

Ya ce, “Mutum 22 ne hatsarin ya rutsa da su. Akwai maza 18, mata biyu, yarinya guda daya da yaro daya.

“Maza 12 da babbar mace daya da yara biyu ne suka rasa rayukansu a nan take.

“Wasu bakwai kuma sun samilu raunuka daban-daban,” in ji shi.

Ya kara da cewa an kai wadanda suka jikkata zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi domin ba su kulawar da ta dace.

Kazalika ya ce an kilkace gawarwarkin wadanda suka rasu a asibitin.

Ya bayyana cewa abin ya faru ne da misalin karfe 3:30 na yamamcin ranar Alhamis sakamakon rashin bin dokokin tuki da kuma gudun wuce sa’a.

Ya umarci masu ababen hawa da su tabbatar da kyawun tayoyinsu da guje wa gudun wuce kima tare da bin dokokin hanya.