✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum 11 sun mutu a hatsarin mota a Ondo

Mutum 11 da hatsarin ya ritsa da su sun riga mu gidan gaskiya

Mutum 11 sun mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a yankin Ore da ke Karamar Hukumar Odigbo a Jihar Ondo.

Hatsarin na ranar Lahadi a cewar wata majiya da lamarin ya faru a kan idonta, ya shafi wata tirela ce da kuma bas ta Marcopollo.

“Hatsarin ya auku ne bayan da tirelar ta yi kokarin bin hannun da ba na ta ba wanda hakan ya sa aka yi taho mu gama da bas din da ke tahowa daga babbar hanyar Benin,” in ji majiyar.

Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadurra na yankin Ore, Sikiru Alonge, ya tabbatar da aukuwar hatsarin.

“Mun kashe wutar da ta kama sakamakon aukuwar hatsarin tare da takaita cinkoson ababen hawa a hanyar,” in ji jami’in.

Jaridar Vanguard ta rawaito duka mutum 11 da hatsarin ya ritsa da su sun riga mu gidan gaskiya sakamakon kunar wuta.