Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa, ta tabbatar da rasuwar aƙalla mutum 10 a wani hatsarin mota da ya auku a ƙauyen Yanfari da ke Ƙaramar Hukumar Taura.
Hatsarin ya auku ne a ranar Talata, 12 ga watan Nuwamba, 2024 a daidai hanyar Kano zuwa Hadejia.
- Abba da manyan mutane za su halarci auren ’yar Kwankwaso a Kano
- Mun biya bashin N63bn da Ganduje ya karɓo — Gwamnatin Kano
Baya ga waɗanda suka rasu, mutum ɗaya ya ji rauni.
Kakakin rundunar, DSP Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da aukuwar hatsarin.
Ya ce lamarin ya auku ne lokacin da wata mota ƙirar bas da ta fito daga Kano zuwa Hadejia ɗauke da fasinjoji 11, ta yi karo da wata tirela.
“Nan take direban motar tare da wasu fasinjoji tara da ya ɗauko suka rasu,” in ji sanarwar.
Tawagar sintiri ta ‘yan sandan Taura sun garzaya zuwa wajen, inda suka ɗauki gawarwakin waɗanda suka rasu zuwa Babban Asibitin Hadejia.
Sun bayyana cewar sauran fasinja guda ɗaya da ya jikkata, yana samun kulawa a cibiyar kiwon lafiya da ke Majia.