✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 10 sun mutu a hatsarin mota a Bauchi

Ya ce daga cikin adadin akwai maza 14, mata biyar, karamin yaro daya sai kuma yara mata biyu.

Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) reshen jihar Bauchi ta tabbatar da rasuwar mutum 10 yayin da karin wasu 12 kuma suka sami munanan raunuka sakamakon wani hatsarin mota a garin Azare na Karamar Hukumar Katagum a jihar.

Hatsarin dai ya faru ne bayan wata motar fasinjoji mallakin Hukumar Sufuri ta Jihar Gombe ta yi taho-mu-gama da wani dan acaba a garin.

Kwamandan hukumar a jihar, Yusuf Abdullahi wanda ya tabbatar da hakan ga ’yan jarida a karshen mako a Bauchi ya kuma ce mutum hudu dake kan babur din dan acaban sun mutu, sai kuma shida daga cikin fasinjojin dake cikin motar mai dauke fasinjoji 18 suma sun riga mu gidan gaskiya.

Ya ce gudun wuce sa’a ne ya haddasa hatsarin.

“Dan acabar ne ya tsallaka ta gaban motar wacce take tafka gudu ita kuma ta bi ta kansa. An kira jami’anmu  a garin Azare, wadanda suka garzaya domin ceto wadanda lamarin ya ritsa da su kuma suka kai su asibit inda likita ya tabbatar da rasuwar 10 daga cikinsu.

“Mutum 22 ne gaba daya hatsarin ya ritsa da su,” inji kwamandan.

Ya ce daga cikin adadin akwai maza 14, mata biyar, karamin yaro daya sai kuma yara mata biyu.

Yusuf ya ce an kai gawawwakin mamatan zuwa sashen ajiyar gawawwaki na Cibiyar Lafiya ta Tarayya dake garin na Azare, yayin da su kuma wadanda suka jikkatan aka kai su sabon dakin shan magani na Jama’are.

Ya shawarci masu amfani da ababen hawa da su rika tuki da cikin natsuwa da lura domin rage yawan hadurran dake lakume rayuka da dukiyoyin jama’a.