✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum 1 ya rasu, 3 sun ji rauni a hatsarin mota

Hadarin ya faru ne sakamakon tsinkewar birkin daya daga cikin motocin.

Hatsarin mota ya yi ajalin wani mutum a kan titin Oshodi, a jihar Legas.

Hadarin ya faru ne sakamakon tsinkewar birkin babbar motar kirar bas, wadda ta yi kan daya motar ta murkushe ta a safiyar Juma’a.

Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Legas (LASEMA), ta isa wajen don kai dauki ga wadanda hadarin ya ritsa da su.

LASEMA ta bayyana cewa mutum daya ya rasa ransa, sannan biyu sun samu raunuka daban-daban kuma jami’an hukumar, sun kai su wani asibiti a yankin na Oshodi.

Wanda ya rasa ransa kuma an ajiye gawarsa a asibitin, kafin ’yan uwansa su dauki gawar.

%d bloggers like this: